GHANA: Yadda Aka Yi Bikin Ranar Hausa Ta Duniya

Bikin Ranar Hausa Ta Duniya A Ghana

Tarihi na nana cewa Hausawa ne suka kafa kusan duk zanguna da suke cikin Ghana. Domin haka ne harshen Hausa ya kasance harshen da ake mu’ammala da shi a matattarar al’ummu da ake cewa Zango a Ghana.

Hausawan da asalinsu daga kasashen Najeriya da Nijar ne, suna samun karbuwa a matsayin ‘yan kasa; haka kuma harshen hausar ke kara bunkasa.

A ranar bukin Hausa ta shekarar da ta gabata, tsohon shugaban kasa, John Dramani Mahama ya tabbatar da gudunmawar da Hausawa suka bayar wajen samun ‘yancin kasar Ghana daga kasar Burtaniya. Haka kuma Hausawa suka ci gaba da ba da gudunmawa wajen ci gaban kasar ta fannoni daban daban. Sai dai duk da haka, Hausawa na fuskantar rashin amincewa daga kabilu da wasu jami’o'in gwamnati, inda ake kwatanta su da cewa ba ‘yan kasa ba ne, duk da cewa sun shigo kasar nan daruruwan shekaru da suka gabata.

Bikin Ranar Hausa Ta Duniya A

Kungiyar matasan hausawan Ghana, Hausa Youth Ghana, ta tashi haikan wajen magance wadannan matsalolin, kuma kamar yadda mai magana da yawun kungiyar, Dan Masanin Sarkin Hausawan Accra, Alhaji Rabiu Maude, hakarsu ta fara cimma ruwa, domin sun yi zama da shugaban hukumar ci gaban Zango, Dakta Abdallah Banda, kuma ya yi musu alkawarin cewa, a duk lokacin da wani Bahaushe ko dan Zango ya fuskanci matsalar matsayin dan kasa, a sanar da su, za su yi maganin abin.

Bikin Ranar Hausa Ta Duniya A Ghana

Duk da tasirin da Hausawa da harshen Hausa ke da shi wajen ci gaba da wayar da kan jama’a, musamman mazauna Zango ta kafofin sadarwa, har yanzu Hausa ba ta cikin manhajar koyarwa a Ghana.

Game da hakan Alhaji Rabiu Maude ya ce, kungiyar ta yi zama da ministan ilimi da kuma ministan yawon bude ido da al’adu, kuma sun tabbatar da cewa za su yi zama kan hakan.

Bikin Ranar Hausa Ta Duniya A Ghana

Sarkin kabilar Basare na Accra, Ibrahim Bawa, ya bayyana tasirin Hausa ga su wadanda ba Hausawa. Yace, shi ba Bahaushe bane, amma da harshen Hausa yake mu’amala a Zango saboda yadda harshen ya kasance kowa shi yake yi.

Yau Asabar 26 ga watan Agusta take ranar Bukin Hausa na Duniya, kuma bukin wannan shekarar na birnin Accra, ya samu halartar mutane daga duk bangarorin kasar; Hausawa da wadanda ba Hausawa ba, kamar yadda Hajiya Hafsat Kadiri English, Gimbiyar Sarkin Hausawan Accra ta ce.

Kamar yadda muke da banbancin karin Hausa; kamar Kananci, zazzaganci, sakkwatanci da sauransu, shin Hausar da ake yi a Ghana za ta samu wannan matsayin kuwa? Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na Jami’ar Sakkwato ya ce:

"Hausar Ghana ta kai a ce akwai Hausar Ghana a ka’ida, domin abin da ke karya harshe shi ne kalmomi mabanbanta; ko hawa da saukar murya ya banbanta a kalma daya, ko ya zamanto akwai furuci na wasu haruffa da za a iya banbanta wani harshe da wani karin harshe, kuma duk akwai su a Ghana."

Saurari rahoton Idris Abdallah:

Your browser doesn’t support HTML5

Bikin Ranar Hausa Ta Duniya A Ghana