Ma'aikatan suna neman a biysu wasu alawunsu ne da suka makale tun bara.
Babu wani ma'aikaci da ya rage a kowace kotu saidai masu tsaro da suke kula da kotunan.
Alkalai da lauyoyi da ma wadanda ake yi masu shari'a sun saura a bayan kaure ne sakamakon yajin aikin da ma'aikatan kotunan suka shiga na gama gari wanda jiya ya shiga rana ta biyu.
Wani lauya yace akwai abubuwa da ya kamata a yi amma ba za'a iya yi ba sabili da yajin aikin. Idan akwai wanda za'a ba beli dole ya cigaba da zama a gidan kaso.Masu gabatar da kara ma basu da daman shiga kowace kotu a halin da ake ciki.
Amma su ma'aikatan kotunan sun ce rashin biyansu hakinsu ya jefasu cikin mawuyacin hali. Wasu an kori 'ya'yansu daga makarantunsu sabili da sun kasa biya. Sun ce basu san abun da zasu yi ba idan ma rance suka karba zasu biya kudin ruwa da dama. Ya zama masu wajibi su fantsama yajin aiki. Wai sun dogara akan alawus din ne wurin biyan kudin gida, ruwa da wuta da dai sauransu.
Shugaban kungiyar ma'aikatan Alex Natty ya mayarda martani akan zargin da ake yi masu na rashin kirki. Yace suna sane da irin matsalar da yajin aikin ka iya haifarwa amma kuma dole ne su nemi mafita daga cikin mawuyacin halin da suka fada. Yace wahalar da suke sha ta fara shafar iyalansu. Saboda haka ya roki jama'a kada su daukesu tamkar mutane ne marasa kirki.
Shi kuwa ministan harkokin kwadago Haruna Idrisu ya kyautata zaton kafin karshen wannan makon za'a samu masalaha kuma ma'aikatan zasu koma bakin aikinsu.
Ga rahoton Yakubu Baba Makeri.
Your browser doesn’t support HTML5