KUMASI, GHANA - Shugaban kamfanin Benjamin Asante, shine ya shedawa manema labarai haka, Ya kuma bayyana cewa, kafin watan Maris din shaikarar 2017 sai wasu Chinisawa su hamsin da biyu ne ke kula da na’urori a kamfanin amma sai aka gano cewa kamata yayi da al’umman kasa su gudanar da wannan aiki.
Dalilin haka suka kulla yarjejeniya da 'yan kasar Chinan da suka amince t su horas da ma'aikatan kasar Ghana su gudanar da ayyukan da takwarorin su na kasar China ke gudanarwa. A yanzu babu ‘dan wata kasa ko daya injiniyoyi dake kula da na’urorin sarrafa iskar gas a kamfanin sai 'yan kasar Ghana.
Shugaban kamfanin ya bayyana cewam tun lokacin da injiniyoyin kasar suka fara wannan aiki kuwa ba'a samu wata matsala ba.
Wannan mataki da gwamnatin Ghana ta dauka ya farantawa al’umma rai sosai inda mai sharhi bisa harkar sufiri akasar kana tsohon wakilin jamiyyan adawa a zauren majalisan dattawa a Ghana Adam Mutawwakil ya ce wannan matakin baiwa al’umman Ghana dama ya da ce sosai tare da baiwa gwamnati shawara cewa duk wata masana'anta da zata fara aiki kamata ya yi a ringa garwaya ‘yan kasa da baki domin al’umman su ci moriyar albashi.
Masana tattalin arziki kuwa sunce baiwa ‘yan kasa damar zai rage matsalar faduwar darajar sidi bisa dalar Amurka inji Mallam Najeeb Ibn Hassan masanin tattalin arziki.
Ghana dai ta shiga cikin jerin kasashen da ke samar da iskar gas a Afrika ta Yamma amma masana sun ce yawan Gas din da ta samar bai kai yadda zai ishi al’ummar fadin kasar da adadin su ya zarta miliyan talatin ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adams:
Your browser doesn’t support HTML5