Tawagar Ghana Blackstars zata fafata ne da kasar Sudan a ranar 12 ga wata na Nuwamba a filin wasan Cape Coast, kana bayan kwanaki biyar kasashen biyu zasu sake raba rana a can kasar Sudan.
A cikin wannan wata ne dai za a soma wasanni cancantar shiga gasar cin kofin Afrika.
Tawagar Blackstars ta yi wasanni sada zumunta na kasa da kasa guda biyu yayin da ta kara da makwabciyarta a Afrika ta Yamma, wato kasar Mali da kuma kasar Qatar a garin Antalya, da ke kasar Turkiya.
Tawagar Blackstars ta sha kashi da ci 3-0 a hannun kasar Mali a ranar tara ga watan Oktoba a filin wasan Emir, amma ta farfado bayan kwanaki uku kacal ta lallasa kasar Qatar da ci 5-1 a filin wasar Titanic.
Kasar Ghana ce ta farko a rukunin shida da maki 6 bayan nasarar da ta samu a kan kasashen Afirka ta Kudu da Sao Tome & Principe, a watan Nuwambar shekarar 2019.
Ga Jerin Sunayen 'Yan wasan
Masu tsaron gida: Richard Ofori (Orlando Pirates FC), Razak Abalora (Asante Kotoko SC), Lawrence Ati-Zigi (St Gallen).
‘Yan wasan baya: Baba Abdul Rahman (Chelsea FC), Gideon Mensah (Vitoria de Guimaraes, Afful Harrison (Columbus Crew FC), Anang Benson (MSK Zilina), Djiku Alexander (Strasbourg FC), John Boye (FC Metz), Nicholas Opoku (Amiens FC), Joseph Aidoo (Celta Vigo).
Masu wasa a tsakiya: Partey Thomas (Arsenal FC), Baba Idrissu (RCD Mallorca), Mubarak Wakaso (Jiangsu Suning FC), Emmanuel Lomotey (Amiens FC).
‘Yan wasan gaba: Andre Ayew (Swansea City FC), Tariq Fosu (Brentford), Samuel Owusu (Al-Ahli Jeddah) Jordan Ayew (Crystal Palace FC), Caleb Ekuban (Trabzonspor), Jamie Leweling (Greuther Furth), John Antwi (Pyramids FC), Jeffery Schlupp (Crystal Palace).