Dangane da shiryen-shiryen tunkarar wasannin lig na kakar shekarar 2020/2021, kungiyar Hearts of Oak tan gani nada dan kasar Portugal Carlos Manuel Vaz Pinto a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasanta zai taimaka mata ainun.
Kungiyar ta sanar da hakan a shafinta na Twitter cewar “Dan kasar Portugal mai horar da ‘yan wasa Carlos Pinto ya shigo cikin iyalin Phobian”
Kungiyar Accra Hearts of Oak ita ce ta lashe kofin zakarun Afrika ko kuma “African Champions League” a shekarar 2000 ta kuma lashe Confederation da kuma Super Champions a shekarar 2000.
A matsayinta na kungiyar da tafi kowace kungiyar kwallon kafa a Ghana, ita ce ta biyu wurin yawan lashe wasan lig din kasar bayan Kumasi Asante Kotoko.
Sabon kocin mai shekaru 46 da haifuwa ya koma kungiyar Hearts of Oak ne bayan kwantiraginsa da kungiyar matasan ‘yan wasan kwallon kafar Fotigalia ta kasar Portugal ‘yan kasa da shekaru 23 ya zo karshe a watan Yunin bana.
Sai dai a baya-bayan nan ya horar da ‘yan wasan wata kungiyar kasar Angola guda biyu da suka hada da C.R.D Libolo da Caala.
Vaz Pinto kuma ya shafe shekara guda a matsayin manajan wata kungiyar kasar Habasha, Saint George SA, a shekarar 2017.
Facebook Forum