A wata sanarwa ta daban, ma’aikatar ta ce bata da wata masaniya akan auna wani dan Ghana a birnin Abuja.
Sanarwar ta ce “Bamu da labarin wata barazana dake auna ‘yan Ghana wadanda ke ci gaba da zaman lafiya da ‘yan uwansu ‘yan Najeriya maza da mata.”
A don haka ma’aikatar harkokin wajen ta yi nadama kana ta roki gafara akan duk wata damuwa da wannan sanarwar ta haifar. Ta kuma ce a yi watsi da wannan sanarwa kwata-kwata.
A watan da ya gabata, Amurka, Birtaniya da wasu kasashen ketare suka fitar da sanarwa, inda suka yi kira ga ‘yan kasarsu da su yi hattara saboda akwai yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a birnin na Abuja.
Hukumomin Najeriya sun yi watsi da sanarwar ta Amurka da Birtaniya kan yiwuwar kai hare-hare a Abuja inda suka ce babu wani abu makamancin haka.
A sanarwar ta jiya Laraba da Ghana take nisanta kanta da ita, ta ce ta dauki wannan mataki ne lura da umarni da hukumomin Najeriya suka ba wasu otel-otel na su rufe harkokinsu. Sanarwar ta kuma ce, “Idan har ya zama dole sai an yi tafiya zuwa birnin na Abuja, akwai bukatar a yi takatsantsan."