Tsokacin al’umman na zuwa ne biyo bayan wata taho-mu-gama tsakanin dakarun soja da wasu matasa a jihar Ashanti a daidai lokacin da sojojin suka kona na’urorin hakar ma’adinai lamarin da ya yi sanadiyar tashin gobara a wani gida dake kusa da wurin da ya k ne kurmus.
Yayin hirarsa da Muryar Amurka Irbad Ibrahim mai sharhi a kan tsaro ya ce kamata ya yi da dakarun soja su sauya salon su wurin yaki da masu hakar ma’adinai ta barauniyar tun da yake kona na’urorin excavators din na haifar da tashin hankali.
Yahaya daya daga cikin masu hakan ma’adinai da manyan na’urorin excavator ya roki gwamnati da ta sauya matakin saboda suna kashe kudade masu dimbin yawa ne wurin sayo na’urar da suke amfani da ita wurin gino da kwashe kasan zinari.
Sai dai kuwa shugaban dakarun soja a yankin jihohin arewa Gabriel Aphor, ya ce matakin da suka dauka na kona na’urorin shine mafita kuma ba kasafai haka suke kona naura ba sai sun tabbatar da ana aiki da ita ta haramtaciyar hanya.
Shi kuwa Alhaji Musah Shekayi daya daga cikin jami’an sadarwa na jami’iyyar NPP mai mulki a Ghana cewa yayi tuni gwamnati ta dakatar da kona na’urorin.
Hakar ma’adinai ta barauniyar hanya na daga cikin abubuwan da ke gurbata ruwan sha da kasar shuka tare da gurbata muhalli kasar Ghana abin da gwamnati ta ce ba zata yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na shawo kan wannan matsala.
Ga dai rahoton Hamza Adam daga birnin Kumasi Ghana:
Your browser doesn’t support HTML5