GHANA: Shugaba Akufo Addo Ya Taya Alummar Musulmai Murnar Babbar Sallar Layya

Sallar Eidi

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo Addo ya ce ya rage albashin sa da na ministocinsa da kashi 30 cikin dari a wani matakin farfado da tattalin arzikin kasar Ghana.

Shugaban ya ce daga cikin dabarun farfado da tattalin arziki kasar ya rage kashe kashe kudade a kan ministoci da hukumomi da kashi 30cikin darin sannan ya kuma rage albashin duk wani ma’aikacin gwamnati da ya nada ciki har da shi kansa, kana ya rage bada man fetur kyauta ga jami'an gwamnati da kashi 50 cikin dari.

Nana Addo Akufo


Shugaban ya fara jawabin sa da sallama ga masu ibada inda ya taya al'ummar Musulmai murnar babban sallar layya daga a filin dandalin independence Square a birnin Accra.

Sallar Eidi


Shugaban Limama kasar Ghana Dr. Usmanu Nuhu Sharubutu ne ya jagoranci Sallar idin inda a cikin hudubar sa ya nunu dalilin yin babban sallar layya da muhimmancin yanka dabbobi da kuma nuna yanda ake yiwa iyaye biyayya.

Sallar Eidi


Duk da cewa bara an samu raguwar barazanar annobar cutar corona a duniya amma duk da hakan ba a yi babban salla layya cikin walwala kamar wasu shekarun baya ba. Jamma’a sun nuna jin dadi hakan da kuma godewa Allah.

Saurari cikakken rahoton Hawawu AbdulKarim:

Your browser doesn’t support HTML5

GHANA: Nana Addo Akufo Ya Taya Alummar Musulmai Murnar Babban Sallar Layya