GHANA: Matsalar Wutar Lantarki Ta Janyo Asarar Tarin Dukiyar Al'umma Da Kamfanoni

Wutar lantarki

Dubban kananan masana'antu ne su ka yi hasarar zunzurutun kudade sakamakon matsalar rashin wuta da suke fuskanta kazalika wasu gidaje sun shafe kwanaki ba tare da wutar lantarki ba.

Hukuma dake da alhakin rarraba hasken wutar lantarki a kasar wato ECG a takaice ta alakanta wannan al'amari da wata tangarda da take fuskanta akan na’urar sayar da wutar lantarki.

Tun ranar talata na makon da ya gabata ne dubban alumar kasar suka koka kan rashin wutar lantarki abinda suka ce yana sanya harkokinsu na yau da kullum cikin halin koma baya.

Wutar lantarki

A hirar shi da Muryar Amurka, Mallam Ishaku mazaunin birnin Kumasi a Ghana ya bayyana cewa,sun shafe kwana uku cikin duhu sakamakon rashin wutar lantarki.

Wutar lantarki

Shi kuwa mai magana da yawun hukumar rarraba hasken wutan lantarki a jahar Accra, Fred Johnson, ya fadawa manema labaru cewa wata tangarda suke fuskanta akan na’urar sayar da wutar lantarki amma suna iya kokarinsu domin shawo kan matsalar.

"muna da sanin wannan matsala kuma mun sanarda injiniyoyinmu suna aiki tukuru domin magance wannan matsala", inji shi.

Dubban al'umma a jihohi goma na kasar ne ke fama da matsalar tun ranar talata kuma a ranar Jumma'a, hukumar tayi alkawarin magance wannan matsala amma har i zuwa lokacin hada rahoton ba ta dauki mataki ba.

Saurari rahoton Hamza Adam:

Your browser doesn’t support HTML5

GHANA: Matsalan Wutan Lantarki Yayi Sanadiyar Asaran Tarin Dukiyar Masana'antu Da Gidaje