GHANA: Ana Zargin Gwamnati da Yiwa Likitoci Rikon Sakainar Kashi

Shugaban Ghana John Dramani Mahama.

Rikicin dake tsakanin gwamnatin Ghana da kungiyar likitocin kasar sai kara rincabewa yake yayiinda har kawo yanzu basu cimma daidaito ba

Yayinda rikicin dake tsakanin gwamnatin kasar Ghana da kungiyar likitocin kasar ke cigaba mutane yanzu sun fara mutuwa saboda rashin likitoci a asibitocin gwamnati.

Kungiyar tana tuhumar gwamnati da yi masu rikon sakainar kashi. Wakazalika kungiyar tace gwamnati bata nuna himmantawa ba wurin tattaunawa da kungiyar akan tsarin aikinsu ba.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar jiya Talata ta zargi gwamnati da gaza tsayar da wakilan din din din a wurin tattaunawar sulhu da suke yi.Kullu yaomin gwamnatin na canza wakilanta lamarin da ya kawo cikas ga ci gaba.

Kungiyar ta zargi gwamnati da aiko da wakilan da ba zasu iya yanke shawara a madadinta ba.

A karshen wata zaman da shugabannin likitocin suka yi a garin Kufureduwa saboda daukan shawara na karshe akan yajin aikin da suke yi na sai baba ya gani shugaban kungiyar likitocin da babban sakatarensu sun saka hannu a wata sanarwa cewa ranar Juma'a mai zuwa 14 ga wannan watan zasu yanke shawararsu ta karshe ko su koma aiki kokuma su ajiye aiki.

Tuni shugaban kasar ta Ghana John Dramani Mahaman ya gargadi likitocin da su koma kan teburin tattaunawa. Yace ya kamata likitocin da gwamnati su cigaba da tattaunawa har a samu masalaha.

Saidai shugaban kasar yace duk abun da zasu cimma dole ya kasance cikin kasafin kudin badi. Yace shi ba zai yadda a kawo batun karin albashi da alawus ba cikin kasafin kudin bana indan bai yi tanadinsa ba.

Yanzu dai ra'ayoyin mutanen kasar sun dare gida biyu. Akwai masu bin ra'ayin likitocin akwai kuma masu bin na gwamnati. To saidai su likitocin suna bayan kungiyarsu daram.

Ga rahoton Yakubu Baba Makeri da karin bayani.