Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matuka Taxi Sunyi Zanga-zanga a Ghana


Buduburam, Ghana.
Buduburam, Ghana.

Yayinda farashin mai yake faduwa a kasuwannin duniya, a kasar Ghana gwamnati ta kara farashin man fetur lamarin da baiyi wa matuka tasi dadi ba.

Dalilin haka ne matukan suka yi zanga-zanga na tsawon sa’o’i biyu, domin bayyana rashin gamsuwarsu da matakin da gwamnati ta dauka.

Shugaban kungiyar ‘yan taxi na birnin Accra, Charles Danso ya nuna damuwarshi yana cewa “ina gani, idan wannan gwamnati har ta isa, mai sauraren talaka ce, ina sane da cewa itace tayi mana alkawari akan wani tsari na musamman, wanda idan aka samu tashin farashin mai a kasuwannin duniya, kai tsaye kudin mai zai tashi a Ghana. Kazalika, idan aka samu raguwa, kudin mai zai ragu.”

“Amma sai gashi, kudin mai ya sauko a duniya, amma gwamnati tayi mana kari, kashi 17 cikin 100 akan mai.”

Sai dai ba ‘yan tasi ne kadai suke nuna damuwarsu ba, masu tuka motoci na gida harma da wadanda basu da motocin, suna kokawa akan tsadar kudin motar haya.

Yaro Kasambata, shine jami’in hulda da jama’a a hukumar man fetur ta kasar Ghana “hukumata baza ta iya cigaba da yin ragowar kudin mai ba, saboda tana so tayi amfani da ragowar kudin mai da aka samu a kasuwannin duniya.

Su dai direbobin tasi, sunce sun zubawa gwamnati idanu domin ganin irin matakin da zata dauka nan gaba, ko zatayi wannan ragi, ko a’a.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG