Matakin shugaban na zuwa ne biyo rahoton da aka wallafa cewa, karamin ministan ya ce sai masu neman zuba jari a Ghana sun bada kimanin dubu dari biyu na dalan Amurka kafin su gana da mataimakin shugaban kasa, abinda ofis din ya yi adawa dashi.
A wata wasikar da ofis din shugaban kasa ta fitar tare da sanya hannun shugaban sashen sadarwa Eugune Arhin, shugaba Nana Addo ya bukaci jami'in da ke gabatar da karar masu yin almubazzaranci da dukiyar kasa wato OSP a takaice da ya fara bincike kan wannan alamari domin ajiye doka a mazauninta.
Sai dai ya yi wa karamin ministan godiya tare da fatan alkhairi biyo bayan ya sallame sa daga mukaminsa.
Wasu masharhanta na ganin wannan matakin korar karamin ministan bai dace ba saboda bai samu dama ya wanke kansa ba.
Shariff Abdul Salam mai sharhi bisa harkar siyasa ta kasa na ganin kamata yayi da shugaban kasa ya saurari bayanin karamin minista tukuna ya dau mataki a kansa.
Shi kuwa babban jami'i a sashen gudanarwa na musamman a ofis din mataimakin shugaban kasa, Ali Suraj ya ce matakin da ofis din shugabancin kasa ya dauka shine mafi a'ala tare da yin adawa bisa zargin cin hanci a ofis din.
Mallam Shuaib Abubakar masanin tattalin arziki a Ghana na ganin wannan rahoton da aka wallafa na iya zamowa izina ga wasu jami'an gwamnati da ke karban cin hanci a hannun masu neman zuba jari a Ghana.
Wasu al’umman Ghana sun gabatar da mabanbantan ra'ayoyinsu game da matakinda shugaban kasa ya dauka na tsige karamin ministan kudin kasar a inda wasu ke cewa hakan ya dace kazalika wasu na ganin akwai wasu da aka yi ma korafi makamantan hakan amma kuwa shugaban kasa bai dau mataki a kansu ba.
Saurari rahoton Hamza Adam:
Your browser doesn’t support HTML5