Taron, wanda aka shirya shi da nufin bunkasa tattalin arziki ta hanyar sana’oi da kasuwanci ga al'ummomin Zanguna a fadin kasar Ghana, ya gudana ne a dakin taro na babban masallacin kasa da ke birnin Accra.
Taron, mai taken: ‘Ƙarfafawa, Hadawa, Sauyawa: Ƙarfafa Ruhin Kasuwancin ‘Yan Zango’ ya hado kan matasa kimanin 500, shugabannin al’umma, masu kananan sana’o’i, masu zuba hannun jari, da masu tsara manufofi, inda aka tattauna dabarun bunkasa cin gaban Zangunan Ghana ta hanyar karawa matasa kwarin gwuiwar gudanar da sana’oi da kasuwanci da kuma bude kananan masana’antu.
Mahmud Jajah, shugaban ‘Zongovation Hub’, kungiyar da ta tsara shirin ya bayyanawa Muryar Amurka game da wannan taro.
Yace: Zangovation Hub kungiya ce ta matasa da take taimakawa matasa samun sana’ar yi. Wannan shirin, shun samu hadin gwuiwa ne da Ma’aikatar harkokin kudi da Bankin Duniya, wanda ke son taimakawa matasa a duniya baki daya, shi ne suka tuttube mu domin muna kokari, sai suka ba mu tallafin baiwa matasa horo har na watanni hudu. Kuma a karshe muka bas u dama don su zo su nunawa duniya abinda (sana’a ko kasuwanci) da suke yi.
Babban bako na musamman a wurin taron, karamin minista kan harkokin kudi, Dokta Mohammed Amin Adam ya shawarci al’ummar Zango; yace:
Mun dade muna barci, kuma ga dukkan alamu an kai ga cewa mu ‘yan Zango muna baya. Amma, ‘yan zangon ba ma baya, domin muna da mutanen da suka ba da gudunmawa wajen ci gaban kasarmu, a matsayinsu na likitoci, malaman makaranta, ‘yan kasuwa da sauransu, amma muna bukatar mu harhado ci gabanmu da kanmu, don da haka ne za mu iya ba da labarin kan mu.
Baya ga shawarwari daga wasu fitattun yan kasuwa, an bude fili ga wasu gungun matasan yan kasuwa 15 inda suka bayyana dabarun yadda za su gudanar da kasuwancinsu kuma su samu riba ga wani kwamiti da zai tantance gungun da ya yi nasara, daga bisani a ba shi tallafin kudi mai tsoka da zai gudanar da kasuwanci. A karshe, gungun da Bushira Abbas dake noman Abarba ne ya yi nasara.
Bushira tace: Muna sana’ar noman Aburba, kuma an ba mu horo na fiye da watanni hudu. An koya mana ababa da yawa, kuma na karu da yawa, har da yadda zan amshi kalubalen dake tattare da kasuwanci na.
Aishatu Yusif, daya daga cikin wadanda suka halarci taron tace ta yi farin ciki da wannan taro domin ta karu kwarai, musamman daga wacce ta yi bayanin sana’ar yin sabulu. Tace, tana da kasuwanci da take yi, amma yanzu za ta gwada yin sana’ar yin sabulun, domin Karin kudaden shiga.
Ita kuma Khadija Ali, ta bayyana farin cikinta da ta ga yaran Zango suna baje kolin sana’oinsu. Tace suna godiya ga Allah, kuma Allah Ya sa su fi haka.
Kungiyar ‘Zongovation Hub’ ce ta shirya taron tare da hadin gwuiwar Bankin Duniya da ta dauki nauyin shirin da Tsarin Harkokin Kasuwanci da kirkire-kirkire na Kasa ko (NEIP), da kuma Ma'aikatar Harkokin Kudi ta Ghana.
Domin karin bayani saurari rahotan Idriss Abdullah.
Your browser doesn’t support HTML5