Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta'adda Sun Kai Hari Bamenda A Ranar Kirsimeti


Hotunan Baya Baya: Hari a Kamaru
Hotunan Baya Baya: Hari a Kamaru

‘Yan ta’adda na kungiyar Ambazonia Defense Forces (ADF) sun dau alhakin wannan hari da aka kai a ranar bikin Kirsimeti da farar safiya.

Wani bam na gargajiya ya lalata wasu shaguna guda uku ba tare da haddasa asarar rayuka ba da sanyin safiyar yau ranar Kirsimeti a tashar T Junction da ke Bamenda a kasar Kamaru.

‘Yan ta’adda na kungiyar Ambazonia Defense Forces (ADF) sun dau alhakin wannan hari da aka kai a ranar bikin Kirsimeti da farar safiya.

‘Yan awaren sun lashi takobi haddasa tashin hankali har sai gwamnatin kasar Kamaru ta amsa bukatunsu gaba daya inji Muntary Hamisu wani mazaunin Bamenda, yana cewa

‘’Su kace suna da wasu bukatu waddanda ya kamata gwamnati ya duba, ya gyara’’, in ji Muntary.

Tun shekarar 2016 ake gwagwarmaya tsakanin ‘yan awaren Ambazonia masu neman ‘yancin kai da sojojin gwamnatin Kamaru kuma yakin ya kasa karewa

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG