Mabiya Addinin kirista a jihar Nejan Najeriya sunyi amfani da bukukuwan kirsimetin wanan shekara ta 2023 wajen janyo hankalin jama'a akan muhimmancin hadin kai da kuma zaman lafiya a Najeriya.
Shugaban Kungiyar Kiristoci ta CAN a jihar Neja, Bishop Bulus Yohanna, yayi amfani da wanan dama wajen bayyana cewa suna bukatar ganin gwanatin Nigeria ta maida hankali wajen dawo da cikakken tsaro ga yan kasa.
“Shawarana shine gwamnati ta manta da manya manyan ayuka. Ta mayar da hankali wurin tsaro. Saboda in ka kaddamar da babban aiki amma babu tsaro, ba abunda ka yi. Tafiyar ma ya zama wahala”, a cewarsa.
Tsohon Kwamishinan Labarai a jihar Nejan, Jonathan Vatsa yace basa goyon bayan yin sulhu da yan ta'adda da suka addabj jama'a ya na cewar '‘akwai wasu manyanmu a Arewa da har yanzu basu yadda sojojinmu su bi su a yi yaki da su ba. Sai dai a yi sulhu.
“A na sulhu da mugun mutum ne? Wanda in ya same ka zai kasheka?” in da ya kara da cewa a bawa sojoji “izini su bisu su nemo inda suke. Sojoji su kai musu hari a duk inda suke. Duk ramuka da suke ciki a fitar da su. Sojojinmu na da karfi amma abunmu a arewa ta shafi addini da kabilanci” in ji shi
Asakonta ga mabiya addinin Kirista a Jihar Gwamnatin Jihar Neja ta bukaci mabiya addinin kristan da su dage da addu'o'i a dai dai wanan lokaci domin dawo da cikakken zaman lafiya a Najeriya,
Duk da yake dai bukukkuwan na Kirsimatin na wannan shekara yazo cikin yanayi na rashin walwala saboda karancin kudade a hannun jama'a dama uwa uba tsadar man fetur da ta addabi yan kasa amma mabiya addinin kirista na cikin yanayi na farin ciki saboda zagayowar wannan rana ta haihuwar Yesu Almasihu.
Dandalin Mu Tattauna