Gbagbo Ya Buya A Dakin Karkashin Kasa A Sa'ilinda Shi Kuma Kwamandan Askarawansa Ke Kiran Da A Tsagaita Wuta

  • Ibrahim Garba

Hayaki kenan ke tashi bisa birnin Abidjan da yaki ya daidaita.

Shugaban dake kan gadon mulki a kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, ya killace kansa cikin wani dakin kankare na karkashin kasa, yayin da sojojin abokin hamayyarsa suka kewaye gidan, amma kuma yace bai shirya mika kai ba tukuna.

Shugaban dake kan gadon mulki a kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, ya killace kansa cikin wani dakin kankare na karkashin kasa, yayin da sojojin abokin hamayyarsa suka kewaye gidan, amma kuma yace bai shirya mika kai ba tukuna.

A cikin wata hirar da yayi ta wayar tarho da gidan telebijin na LCI na Faransa, Mr. Gbagbo yace lallai shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a Ivory Coast a watan Nuwamba. Yace ba zai amince da Alassane Ouattara a zaman shugaban kasar ba. Wannan furuci nasa ya zo a bayan da jami’an gwamnatinsa da na diflomasiyya a Ivory Coast suka ce Mr. Gbagbo yana tattauna ka’idojin saukarsa daga kan mulki.

Suka ce an ci gaba da tattaunawa har cikin daren talata agogon kasar, yayin da shugaban ya killace kansa da iyalinsa a wannan dakin karkashin kasa. Akasarin kasashen duniya sun amince da Mr. Ouattara a zaman mutumin da ya lashe zaben shugaban kasa na watan Nuwamba. Ministan harkokin wajen Faransa, Alan Juppe, yace Faransa da Majalisar Dinkin Duniya su na son Mr. Gbagbo ya rattaba hannu a kan takarda inda zai amince ya sauka daga kan mulki, ya kuma amince da Mr. Ouattara a zaman shugaban kasar.

Kakakin ofishin gudanar da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast, Hamadoun Toure, ya fadawa VOA cewa idan Mr. Gbagbo yana son mika kai, majalisar zata taimaka wajen kare lafiyarsa. Mayaka masu goyon bayan Ouattara sun kwace akasarin yankunan kasar Ivory Coast cikin mako guda kacal. Fada ya yi sauki jiya talata a Abidjan. Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast ya ce wasu manyan janar-janar guda 3 na Gbagbo sun kira majalisar ta waya su na fadin cewa sun umurci sojojinsu da su ajiye makamansu, su mika su ga Majalisar Dinkin Duniya.

Daya daga cikin wadannan manyan hafsoshin soja uku shi ne babban hafsan hafsoshin sojan Mr. Gbagbo, janar Philippe Mangou, wanda tun farko ya nemi da a tsagaita wuta.