Gwamnatin kasar Sudan ta zargi Israila da kaddamar da wani mummunan harin jirgin sama a kan wata mota a jiya talata a gabashin kasar, ta bangaren gabar tekun Maliya.
Ministan harakokin waje Ali Ahmad Karti ya ce Sudan ta tabbata, babu shakka Israila ce ta kaddamar da harin wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu a kusa da filin jirgin saman birnin Port Sudan.
Jami'ai sun yi bayanan da su ka sha bamban da juna game da harin jirgin saman ; 'yan sanda na cewa harin makami mai linzami ne, a yayin da kuma wani jami'in gwamnati ke cewa bom wani jirgin saman wata kasar waje ya saki.
Ba a tantance ko su wanene mutanen biyu da ke cikin motar da aka kaiwa harin ba, kuma Israila ta yi gum da bakin ta, ba ta ce uffan ba game da zargin da ministan harakokin wajen kasar Sudan ya yi ma ta.
A cikin watan janairun shekarar dubu biyu da tara ma, wani jirgin saman da ba a tantance ba ya kai hari kan ayarin wasu 'yan fasa kwauri a wannan jahar ta bakin tekun kasar Sudan.
Mujallar Amurka mai suna Time ta bada labarin cewa Israila ta kai harin ne domin ta hana shigar da wasu makamai zuwa Gaza. Jami'an gwamnatin Israila ba su ce ta tafar ba balle sauke game da harin bom din