Dakarun dake goyon bayan bijirarren shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo sun kai hari kan wani otel inda abokin hamayyarsa, mutumin da kasashen duniya suka dauka a matsayin halaltaccen shugaban kasa Alassane Quattara yake zaune, tunda aka fara takaddama kan zaben shugaban kasar. Kakakin Majalisar Dinkin Duniya yace maharan sun kai harin kwansan bom jiya asabar a otel din Golf dake Abidjan babban birnin kasar. Bisa ga cewarsa, an kai harin ne kusa da fadar shugaban kasa inda Mr. Gbagbo yake boye karkashin kasa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya yi allah wadai da harin na jiya asabar da cewa yanzu ya nuna karara cewa, yunkurin tattaunawar da Mr. Gbagbo ya yi yaudara ce kawai domin ya sake hada kan dakarunsa da kuma basu makamai. Majalisar Dinkin Duniya tayi zargin cewa, dakarun dake goyon bayan Mr. Gbagbo sun yi amfani da tsagaita wutar da aka yi da nufin wanzar da zaman lafiya wajen sake kwace ikon Abidjan.
Dakarun dake goyon bayan bijirarren shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo sun kai hari kan wani otel inda abokin hamayyarsa Alassane Quattara ke da zama,