Gawar Dan Jaridar Da Ya Mutu A Qatar Ta Iso Amurka

Marigayi Grant Wahl ranar 29 ga watan Nuwamba a Qatar (Brendan Moran, FIFA via AP)

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Ned Price, ya ce babu wani abu da ke nuna cewa akwai wata alamar tambaya kan mutuwar dan jaridan, yana mai cewa hukumomin Qatar na ba Amurka hadin kai a binciken da ake yi.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce gawar dan jaridar nan ba’Amurke da ke dauko rahoton wasanni ta iso Amurka daga birnin Qatar.

A makon da ya gabata, Grant Wahl ya rasu yayin da yake aikin dauko rahotanni daga kasar Qatar da ke karbar bakuncin gasar cin kofin duniya.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce, an iso da gawar ne Wahl ta filin tashin jirage na John F. Kennedy da ne New York da misalin karfe takwas na safe agogon gabashin Amurka.

Dan jaridar ya yanke jiki ya fadi ne a ranar Juma’ar da ta gabata, yayin da Argentina da Netherlands ke karawa.