Shugaban kasa Bola Tinubu ya yabawa irin kwazon da Tawagar Super Eagles ta nuna a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar afrika (AFCON) data gudana a kasar Ivory Coast.
Washington DC —
Duk da rashin nasarar da suka yi a hannun masu masaukin baki, Tinubu yace Super Eagles ta nuna kwarewa da jajircewa a gasar.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hadimin shugaban kasar akan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar a lahadin data gabata.
Ivory Coast ce tayi nasara a wasan karshe na gasar afcon ta 2023 bayan data doke takwararta ta super eagles da ci 2 da 1.
Tinubu ya kara da cewar tawagar Najeriyar ta samu gagarumar nasara a idanun al’ummar nahiyar Afrika dama duniya baki daya.
A cewar sanarwar, Shugaba Bola Tinubu ya yabawa tawagar Super Eagles saboda irin kwazon da suka nuna a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika data gudana a kasar Ivory Coast.