Najeriya ne ta fara zura kwallo bayan da mai tsaron baya, Williams Troost Ekong ya farke saura minti 7 kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Ama a minti 63, masaukin bakin suka rama, inda Franck Kessie ya zura wa Kwaddebuwa.
Najeriya ta canja dan wansan tsakiya nan Samuel Chuwkueze da Moses Simon a minti na 56 sannan Kwaddebuwa ta canja 'yan wasa biyu.
Stephane Singo ya karbi Serge Aurier sannan Max Gradel ya maye gurbin Oumar Diakite a baya da tsakiya.
Sai dai a miniti na 81 Sebastien Haller ya zura kwallo na biyu wa masaukin bakin.
Najeriya ta sake sauya 'yan wasantaa minti na 86, a yayin da Joe Aribo ya maye gurbin Zaidu Sanusi, Terem Moffi ma ya maye gurbin Frank Onyeka a karawar a minti na 86.
Kwaddebuwan ta yi nasara ne bayan an kara akalla minti 8 a wasan, inda aka tashi ci 2-1
Dandalin Mu Tattauna