Ana iya tabattar da haka idan aka yi la’akari da abubuwan dake faruwa musamman a jihar Bauchi, ga misali, a cikin yan makonnin nan inda 'yan ta'adda suka kaddamar da harbe harben kan mai uwa da wabi a kasuwanni da gidajen mutane da a wasu lokutan kan janyo rasa rayukan mutane.
Lamarin satar mutanen don neman kudin fansa ba wai ya tsaya kan talakawa bane kawai, kusan za’a ce masu sace sacen mutanen a halin yanzu sun fi maida hankali ne ga masu sarautu da kuma yan kasuwa domin samun saukin neman biyan bukatunsu.
Idan za’a iya tunawa, a kwanakin baya 'yan bindigan sun sace wani hakimi a karamar hukumar Ningi har sai da aka biya kudin fansa naira miliyan biyar da wasu kayayyakin bukatun yau da kullum suka sako shi.
Haka ma yan bindigar sun sace wani dan kasuwar a karamar hukumar Jama’are, inda suka karbi naira miliyan ashirin kafin suka sako shi.
Ko da a kwanan baya ma, rundunan 'yan sandan jihar Bauchin ta gabatar da wasu mutane goma da ake tuhumarsu da fashi da makami da kuma satar mutane da shanu.
Al'amari na baya bayan nan shine satar wani dan kasuwa dan kabilar Ibo da aka yi a kauyen Ganji, cikin karamar hukumar Ningi mai wani suna Daniel da kuma Alhaji Yahaya dake a hannun yan bindigar suna bukatar naira miliyan goma kafin su sako shi.
Malam Kabir Mahmud Abdullahi, wanda shine darekta mai kula da fannin mulki a karamar hukumar Ningi, yayi karin bayani a hirar shi ta wayar tarho inda ya ce suna daukar matakai wajen magance matsalar tsar, wanda ya fi aukuwa lokacin damina.
Wani mai sharhi a Fannin tsaro , Air comodo, Tijjani Baba Gamawa, yace 'yan bindigar da suke yankunan Zamfara da na Dajin Falgure su ne suka shigo jihar Bauchi.
Duk kokarin jin tabakin kakakin hukumar 'yan sanda, SP Wakil ya ci tura.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5