Mazauna garin Jakana dake karamar hukumar Konduga a jihar Borno sun kokawa gwamnan akan matsalar ruwan sha da suke fama dashi shekara da shekaru.
Gwamnan ya ziyarci garin ne saboda duba wasu ayyuka da gwamnatin ke aiwatarwa. Yayinda ya isa garin daruruwan mutane da suka hada da maza da mata da yara suka fito suna kokawa akan rashin ruwan sha.
Jama'ar garin sun ce suna sayen ruwa galan daya daga nera hamsin zuwa dari.
Amma nan take gwamna Kashim Shettima ya yiwa mutanen alkawarin magance masu matsalar inda ya bada umurnin tona masu sabuwar rijiyar bututu. Nan take kuma aka kawo injinan tona rijiyar.
Gwamnan ya cigaba dacewa banda ruwan sha zasu cigaba da gina makarantu da samar masu ababen rayuwa na yau da kullum.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5