Garin Goma Na Kwango Yana Fuskantar Barazanar ‘Yan Tawaye Yayin Da Dubbai Ke Tserewa

Your browser doesn’t support HTML5

Garin Goma Na Kwango Yana Fuskantar Barazanar ‘Yan Tawaye Yayin Da Dubbai Ke Tserewa

Wani makamin roka ya fada kusa da wata jami'a a birnin Goma na kasar Kwango a ranar Laraba yayin da wasu dubban fararen hula suka tsere daga wani sabon hare-hare na 'yan tawayen M23 wanda ke barazanar dukufar da cibiyar babban birnin kasar da ke fama da tashe-tashen hankula a gabashin kasar.

WASHINGTON, D. C. - Kawo yanzu dai ba a samu asarar rai ba sakamakon wannan harin wanda ya fasa wani rami a wani fili da ke unguwar Lac Vert a arewa maso yammacin birnin na Goma, sai dai harin ya nuna irin barazanar da ke iya yi wa birnin mai kusan mutane miliyan biyu.

CONGO

"Wannan ya nuna cewa kungiyar ta M23 na kai hari a Goma ne yanzu, domin kashe mutane a Goma. Dole ne gwamnati ta yi wani abu don hana ci gaban M23," in ji daliba Sophonie Bayonga 'yar shekara 25 a wurin.

A yankin da tuni ke fama da tashe-tashen hankula na 'yan bindiga, 'yan tawayen M23 sun kaddamar da wani sabon farmaki a cikin watan Maris din shekarar 2022, wanda ya haifar da rikicin da ya kai ga shiga tsakani na soji da kuma kokarin shiga tsakanin shugabannin yankin gabashin Afirka. Duk da cewa sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a bara amma an sha keta ta.

CONGO

CONGO

A baya-bayan nan dai rikici ya barke tsakanin ‘yan tawaye da dakarun soji da kungiyoyin kare kai da ke goyon bayansu, lamarin da ya tilastawa daukacin al’ummun yankunan Masisi da Rutshuru tserewa zuwa yankunan da ake ganin sun fi samun tsaro a wajen birnin Goma.

Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a wannan mako dai ta yi alkawarin cewa ba za ta bar Goma da ke tafkin Kivu kusa da kan iyaka da Rwanda ya fada hannun ‘yan kungiyar M23 ba.

-Reuters