Shugabar kungiyar rajin kiran ceto daliban Chibok Dakta Obiageli Ezekwesili ta furta cewa dole su ci gaba da gwagwarmaya ya hanyar nunawa gwamnati kurakurai da zarar sun gano su. Saboda haka suna kan bakan sun a bin diddikin ganin an sako ‘yan matan nan na garin Chibok da aka sace tun kwanaki 594 da suka shude.
Tun wancan lokaci ne tawagar masu rajin ganin an dawo da ‘yan matan suka kafa kahon zukar tarurruka da zanaga-zangar lumana daban-daban don ganin haka ta cimma ruwa, amma sai gashi shekaru biyu na nema haduwa ba tare da jin duriyarsu ba.
Asali ma dai mutane da yawa suna has ashen kila ‘yan matan nan kanana da ake amfani da wasun su wajen tayar da bama baman kunar bakin wake ta yiwu wasun su ne ake tursasawa ko kuma aka juya tunaninsu suka rikide.
Shima wani dan rajin kare hakkin matasa Kwamrade Ibrahim Garba Wala cewa yayi Allah ne kadai yasa yadda zata kaya game da ceto ‘yan matan na Chibok. domin kuwa ko sojojin da ke bakin daga yace ba zaka ji suna cewa ga ranar da za su gano yaran ba.
IG Wala ya bayyana yadda suka ga garin Chibok ya zama abin tausayi musamman yadda mutane suke a takure a dalilan harkokin sintiri masu alaka da tsaro a yankin. Shima Kanar Rabe Abubakar daraktan yada labaran rundunar tsaro sojojin yace, daga ‘yan matan Chibok har ma wadanda bas u ba da aka yi garkuwa dasu yana sa ran da sannu za su ceto su.
Your browser doesn’t support HTML5