Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sauyin Yanayi Ya Jawo Bala'o'i da Yawa - MDD


Shugabannin Duniya a Taron Sauyin Yanayi
Shugabannin Duniya a Taron Sauyin Yanayi

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) mai kula da rage aukuwar canjin yanayi ya fitar da wani rahoto da yace cikin shekaru goma da suka gabata bala'o'i dubu shida da dari hudu da hamsin da bakwai suka faru sanadiyar canjin yanayi.

Sakamakon ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa da fari da sauran ababen dake da alaka kai tsaye da sauyin yanayi suka jawo bala'o'in da hadura.

Farfasa Alhassan Mamman Muhammad na Jami'ar Abuja ya yi bayani akan sauyin yanayi. Yace sauyin yanayi kan sa ruwan tafki ya ragu ko kuma rafi ya kafe gaba daya.

Cikin wani rahoto da ta kira yadda dan Adam ya dandana kudarsa saboda sauyin yanayi Majalisar Dinkin Duniya (MDD) tace daga shekarar 2005 zuwa watan Augustan wannan shekara kimanin mutane dubu dari shida ne suka rasa rayukansu saboda canjin yanayi yayinda kuma mutane biliyan daya da miliyan daya ko sun ji rauni ko kuma sun rasa gidajensu a duk fadin duniya.

Farfasa Alhassan ya bayyana abubuwan da kan haddasa canjin yanayi. Fannin kimiya da fasaha da sinadari da ake kerawa domin jin dadin rayuwa su kan kara dumamar yanayi. Misali iskar da shuka ke fitarwa ita muke shaka yayinda su kuma suna shakar wadda muk fitarwa ta yadda muke nunfashi.

Aikace aikacen kamfanonin dake hako man fetur na taka rawa gaya wurin sauyawar yanayi.

Yanzu dai ana taron canjin yanayi a kasar Faransa inda shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kasance cikin masu halartar taron.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG