Gargadin Amurka ga ‘yan kasarta dake a Mali

  • Aliyu Mustapha
Amurka na jan kunnen Amurkawan da ke kasar Mali da su kwana da sanin cewa mai yiyuwa ne al-Qaida za ta kai hare-hare a inda suke.

Gwamnatin Amurka na yin kashedi ga Amurkawan da ke kasar Mali da su kwana da sanin cewa akwai yiwuwar cewa kungiyar al-Qaidar yankin za ta kai hare-hare. Ma’aikatar harakokin wajen Amurka ta fada a yau alhamis cewa mai yiwuwa ne kungiyar al-Qaidar yankin arewacin Afirka ta kai hari kan duk wani dan wata kasar yammacin duniyar da ya gilma a zaman maida martani ga rawar da Faranshi ta taka kwanan nan cikin wani harin da aka kaiwa kungiyar haka kwatsam har aka kashe ma ta mutane shidda. Harin da aka kaddamar daga kasar Mauritania, wani yunkuri ne da ya ci tura na neman kubutar da wani dan kasar Faranshin da aka yi garkuwa da shi wanda daga bisani kungiyar ta kashe shi. Kashedin da Amurkar ta yi, ya ce har yanzu kungiyar na da sha’awar sace ‘yan kasashen yammacin duniyan da tafiya ta kai kan iyakar Mali da Nijer da Burkina Faso har ma zuwa Bamako babban birnin kasar Mali. A cikin wani sakon jan hankali, ofishin jakadancin Amurka ya ce ya kamata Amurkawa su yi kaffa-kaffa iyakacin iyawar su kuma su guji nuna kai.