Jami’an kungiyar Taliban sun ce sun kama wadansu sojojin Amurka guda biyu a lardin Logar dake gabashin Afghanistan. Kungiyar ta yi wannan harsashen ne yau asabar. Kamfanin dillancin labarai na Reuters kuma ya laburta cewa, gidajen radiyon kasar suna yayata cewa Amurka tayi tayin biyan dala dubu 20 da zumar samun bayanan da zasu kai ga sakin sojojin. Jami’an kungiyar tsaro ta NATO a Afghanistan basu maida martani dangane da wannan harsashen ba. Tun farko jami’an kungiyar tsaro ta NATO sun ce an kashe sojojin Amurka biyar a wadansu hare haren bom biyu dabam dabam da aka kai a kudancin Afghanistan inda dakarun ke kara kaimin kaiwa kungiyar Taliban farmaki. Cibiyar kula da harkokin tsaro ta kasa da kasa ta bayyana yau asabar cewa hudu daga cikin sojojin sun gamu da ajalinsu ne sakamakon tarwatsewar nakiya da aka harhada da hannu da kungiyar Taliban take yawan amfani da su. Daga baya kuma kungiyar tsaro ta NATO ta sanar da mutuwar soja na biyar a wani harin na dabam. Babu kungiyar da ta dauki alhakin hare haren. Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana jiya jumma’a cewa shirin gwamnatin kasar Afghanistan na karbar ayyukan tsaron kasar cikin shekara ta dubu biyu da goma sha hudu , da inganta harkokin mulki da kuma yaki da cin hanci da rashawa, shiri ne dake tattare da gagarumar kalubala. Mr. Ban ya bayyana haka ne a jawabinsa ga kwamitin sulhu na MDD a taron kasashe masu bada tallafi na kasa da kasa da ya jagoranta a Kabul farkon wannan makon da aka gudanar kan makomar kasar Afghanistan.
Jami’an kungiyar Taliban sun ce sun kama wadansu sojojin Amurka guda biyu a lardin Logar dake gabashin Afghanistan.