Jumma’a ce kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’a kara wa’adin aiki na shekara daya,ga rundunar kiyaye zaman lafiya ta hadin guiwa tsakannin ta da Tarayyar Afirka, a yankin Darfur na Sudan, mai fama da rigingimu. Kwamitin ya bukaci dakarun su mai da hankali wajen kare farar hula da ake rutsawa dasu, da kuma masu aikin agaji.
Haka kuma kwamitin ya yi Allah wadai da ci gaba da kai hare hare kan rundunar kiyaye zaman lafiya mai dakaru kusan dubu ashirin da daya.
A farkon makon nan ne jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya,Susan Rice, ta bayyana matukar damuwa, ganin yadda lamarin tsaro yake kara tabarbarewa a yankin na Darfur. Daga nan ta bukaci a magance lamarin ba tare da bata lokaci ba.