Gareth Southgate Yayi Murabus Daga Zama Kociyan Ingila

England manager Gareth Southgate celebrates after the victory over Denmark on July 7, 2021.

Southgate ya karbi ragamar gudanar da Ingila a 2016 lokacin da tawagar ke cikin mawuyacin hali.

Gareth Southgate ya bayyana cewar ya yi murabus daga zama kociyan tawagar kwallon kafar Ingila kwanaki 2 bayan da kasar tayi rashin nasara a hannun Sifaniya a wasan karshe na gasar kasashen nahiyar Turai ta bana Euro 2024.

Sanarwar da ya fitar tace, “lokaci ya yi na samun sauyi, da bude sabon shafi. karawar karshe da muka yi a birnin Berlin da kasar Sifaniya a Lahadi da ta gabata ita za ta ta kasance karshe a matsayin kociyan Ingila.”

Southgate ya karbi ragamar gudanar da Ingila a 2016 lokacin da tawagar ke cikin mawuyacin hali.

A gasa guda 4 da ya jagoranta ya jagoranci Ingila zuwa wasan daf dana karshe sau 3 da wasannin karshe 2.