Gangaminmu Ne Ya Sa Shugaba Buhari Ya Dawo -Adeyanju

Zanga zanga suna bukatar ko Shugaba Buhari ya dawo daga London ko ya yi murabus

Shugaban kungiyar da ta yi gangami da zaman dirshan na kusan makonni biyu a Abuja cewa ko shugaba Buhari ya dawo gida daga London ko kuma ya yi murabus ya ce gangaminsu ne ya dawo da shugaban

Deji Adeyanju ya bayyana kansa a matsayin shugaban kungiyar Concerned Nigerians, kungiyar da ta yi gangami akan ko Shugaba Buhari ya dawo ko ya yi murabus tare da cigaba da zaman dirshan har sai ranar da bukatarsu ta biya.

Akan dalilin da suka yi anfani da kalma 'mumu' yace duk 'yan Najeriya da shugabannin da talkawan su ne "mumu". Injishi, idan shugabanni na sata 'yan kasa suka yi shuru suna kallo sun zama 'mumu'. Yayinda shugaban kasa ya je London jinya bai dawo gida ba kwana da kwanaki, 'yan kasar sun zama 'mumu' Yana mai cewa an dade ana cin zalin 'yan Najeriya tare da nuna masu ko basu da wayo ko kuwa basu da hankali ne. Saboda haka ne kungiyarsa tace "our mumu don do" ma'ana, rashin hankalinmu ko rashin wayonmu ya isa haka.

Yanzu a cewar Adeyanju sun godewa Allah shugaban ya dawo. Wai da basu yi gangamin ba da shugaban bai dawo ba yanzu, watakila ma ya yi kwanaki 300. Adeyanju yace dawowarsa zata sa a yi aiki yanzu musamman ma batun yaki da cin hanci da rashawa.

Adeyanju yace yanzu sun gama aikinsu kuma suna yi ma Shugaban kasa barka da dawowa,da fatan zai yiwa kasar aiki.

Dangane da gangamin nasu, yace 'yansanda sun ci zarafinsu. Sun daddakesu, sun yi kaca kaca dasu.

A cewar Adeyanju mutane goma zuwa ishirin ne suke rikitar da gwamnatin Buhari.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gangaminmu Ne Ya Sa Shugaba Buhari Ya Dawo -Adeyanju - 3' 48"