Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Marawa Shugaba Buhari Baya Sun Yi Gangami a Abuja


Masu gangamin marawa shugaba Buhari baya
Masu gangamin marawa shugaba Buhari baya

Farkon makon jiya ne wasu suka fantsama titunan Abuja suna kiran shugaba Buhari ya dawo gida ko kuma ya yi murabus lamarin da ya harzuka magoya bayansa shirya nasu gangamin wanda suka cigaba dashi yau

Masu marawa shugaban Najeriya baya Muhammad Buhari sun fito yin gangami ne da kade kade da wake wake.

Gagamin nasu na yau ya zo ne bayan da shugaba Buhari ya kwashe fiye da kwanaki casa'in yana karbar jinya a birnin London kasar Birtaniya.

Mukarrabin shugaban masu gangamin Yau Bakan Daura yana mai cewa makircin da aka kulla, su talakawan kasa sun sani kuma Allah Ya fi karfinsu. Yace idan Allah Ya yadda dashi zasu yi sallah. Yace Buhari ya samu lafiya illa dai yana bin umurnin likitocinsa ne kuma da za sun amince masa zai dawo gida Najeriya.

Abubakar Daura yace duk dan Najeriya mai kyakyawar manufa ya san cewa Shugaba Muhammad Buhari yana iyakar kokarinshi. Yana son kasar ta kasance kan turba mai kyau.

Baba Gana Fantami matashi ne dake nuna shugaba Buhari ya kawowa kasar salama. A cewarsa lokacin mulkin PDP mutum bai isa ya kama hanyar zuwa Maiduguri ba daga Kano amma sallar da ta wuce ya tashi daga Abuja da yamma ya tafi Kano daga can kuma sai Maiduguri.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Kaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG