Daga bisa alamu kawunan 'yan Najeriya ya rabu akan Shugaba Buhari saboda suna bayyana ra'ayoyin dake cin karo da juna yayinda suke zanga zanga kullum a Abuja.
Yau wani gungun matasa ya bayyana a karkashin kungiyar Good Governance and Change Initiative ko GGCI. Sun fito sun yi tasu zanga zangar ta nuna goyon bayansu wa Shugaba Buhari.
Kwamred Tijjani Abdulmummuni shugaban kungiyar yana mai cewa abun da su keyi shi ne jawo hankalin matasan Najeriya akan wadanda suke zaman dirshan suna son Shugaba Buhari ya yi murabus wai domin ya dade yana jinya a Ingila, ya yi fiye da kwana 90. Tijjani yace kada a ce mashi ya dawo ko ya sauka. A barshi har ya samu lafiya ya dawo ya cigaba da aikinsa.
Ya cigaba da cewa kasar tana zaman lafiya kuma mukaddashinsa na gudanar da mulkin kasar yadda ya kamata. Ya kira 'yan Najeriya su hada kai su kuma cigaba da yiwa shugaban kasa addu'a.
A wani bangaren kuwa yau kwana hudu ke nan da wasu matasan suka soma zanga zangar kiran Shugaba Buhari ya sauka daga mukaminsa kuma tun lokacin suka cigaba da zaman dirshan. Adeyanju shugaban masu zaman dirshan din yace bai kamata ma sai an roki shugaban ya bar mulki ba. Abun da yakamata ya yi ne.
Barrister Ibrahim Tukur El-Sudi ya tabbatar cewa tsarin mulkin Najeriya bai takaita lokacin da shugaban kasa zai yi yana neman jinya ba muddin ya bayar da sanarwa a rubuce ga majalisar dattawa. Kuma shugaban yayi hakan. Saboda haka duk wani zaman dirshan domin a tilasta masa ya yi murabus aikin banza ne, harara ce a duhu kawai.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Facebook Forum