Ganawar Jakadan Faransa Da 'Yan Takara Ta Janyo Cece Ku Ce

Masu Aikin Sa Ido a Zaben Nijar Daga Kasashen Afirka.

An shiga cece kuce a Jamhuriyar Nijar bayan da jakadan kasar Faransa ya kai ziyara a gidajen ‘yan takarar da zasu fafata a zagaye na 2 na zaben shugaban kasa da za a gudanar ranar 21 ga watan Fabrairu.

Yayinda wasu ke yabawa da wannan ziyara wasu na kallon abin tamkar katsalandan ne a sha’anin zaben kasar.

Ziyarar wace aka yi a asirce labarinta ya bayyana a fili ne bayan da ofishin jakadancin Faransa ya rubuta a shafinsa na facebook cewa jakada Alexandre Garçia ya kai ziyara a gidan dan takarar RDR Canji Mahaman Ousman kafin a washegari ya ziyarci gidan dan takarar PNDS Tarayya Mohamed Bazoum sai dai kuma ba a fadi abubuwan da suka tantauna akai ba, abinda ya sa wasu ‘yan kasa ke ganin ba za a rasa wata boyayyiyar magana ba a karkashin wannan ganawa.

Hukumar Zaben Nijar

Sai dai Bana Ibrahim mamba a kwamitin yakin zaben Mahaman Ousman ya bayyana cewa, ziyarar ba ta rasa nasaba da korafin da a ke yi cewa, kasar Faransa na neman yin katsalandan a zaben na Jamhuriyar Nijar, ya kuma bayyana cewa, dangantakar diplomasiya da ke tsakanin Nijar da kasar Faransa ta bada damar yin irin wannan ganawa.

A hirarshi da Muryar Amurka, shima Kakakin jam’iyar PNDS Tarayya Assoumana Mahamadou ya bayyana cewa wannan ganawa dadediyar al’ada ce da ta samo tushe shekaru aru-aru.

A na shi bayanin, Moussa Tchangari shugaban kungiyar AEC ya ce mai yiwuwa suna neman tabbatacin zaman lafiya ne bayan zabe kasancewa kasar Faransa tana da kaddarori da dama a jamhuriyar Nijar.

jami-an-hukumar-zaben-nijer-sun-gana-da-jakadun-kasashen-waje

nijar-ana-wayar-da-kan-jama-a-kan-zagaye-na-biyu-na-zabe

a-karon-farko-jam-iyyun-adawa-a-nijar-sun-aika-da-wakilansu-hukumar-zabe

Kasar Faransa wace ta yiwa jamhuriyar Nijer mulkin mallaka ta shafe shekaru kusan 50 ta na hakar karfen uranium a yankin Agadez yayinda a yanzu haka wasu sojojinta ke girke a wannan kasa da sunan yaki da ta’addanci abinda ya janyo suka daga wajen kungiyoyin fafitika saboda a cewarsu matakin wani sabon salo ne na mulkin mallaka a dai dai lokacin da ake fadi tashin ganin an watsar da kudaden cfa masu alaka da siyasar tattalin arzikin Faransa a kasashen da ta yiwa mulkin mallaka.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Ganawar Jakadan Faransa Da 'Yan Takara Ta Janyo Cece Ku Ce: 3:00"