Gambia: An Kammala Zaman Sauraron Ra'ayin Jama'a Kan Mulkin Yahya Jammeh

Jerin masu gabatar da shaidu sun kammala bayar da ba’hasi ranar Jumma’a, inda su ka yi ta bayyana yadda aka yi ta tafka almundahana, da kama mutane ba bisa ka’ida ba.

Kwamitin bin diddigin gaskiya da sasantawa na kasar Gambia, ya kammala zamansa na bainar jama’a wanda ya shafe shekaru biyu ya na yi, game da zargin keta hakkin dan adam, wanda aka tafka a tsawon shekaru 22 da tsohon Shugaba mai kama karya, Yahya Jammeh, ya yi a gadon mulki.

Jerin masu gabatar da shaidu sun kammala bayar da ba’hasi ranar Jumma’a, inda su ka yi ta bayyana yadda aka yi ta tafka almundahana, da kama mutane ba bisa ka’ida ba, da kuntata ma mutane, da kashe kashen mutane, wani sa’in ma har ciyar da kadoji aka yi ta yi da gawarwakinsu.

Karin bayani akan: Equatorial Guinea, Yammacin Afirka da Gambia.

Jammeh ya hau karagar mulki ta wajen wani juyin mulkin soji da ya yi a 1994, ya mulki wannan karamar kasa ta Yammacin Afirka har zuwa lokacin da Adama Barrow ya kada shi a zaben watan Disamba na 2016. Jammeh, wanda ke da shekaru 56 yanzu, ya tsere da matarsa zuwa kasar Equatorial Guinea.