Future Prowess Makarantar Marayu Dake Maiduguri Ta Kara Dalibai Dari Uku

'Yan Makarantar Future Prowess marayu dake Maiduguri

A shekarar 2007 ne Barrister Zannan Mustapha ya kafa wata makaranta mai suna Future Prowess domin taimakawa marayu wadda ta yi fice har Majalisar Dinkin Duniya ta ba shi lambar yabo da kyautar kudi Nera milyan 54 lamarin da ya sa ya kara dalibai 300 tare da taimakawa iyayensu.

Makarantar da ake kira Future Prowess dake Maiduguri da aka kafa a shekarar 2007 inda ake koyas da marayu ta fara ne da dalibai 36 a wannan shekarar.

Rikicin Boko Haram ya haifar da karuwan marayu inda suka kai har dari takwas. Daliban sun fito ne daga garuruwa daban daban da ma wasu jihohin.

Makarantar da Barrister Zannan Mustapha ya gina ta yi fice a jihar Borno abun da ya yi sanadiyar jawo hankalin Majalisar Dinkin Duniya har ma ta ba shi lambar yabo da kudi Nera miliyan 54.

Sanadiyar kyautar da aka ba shi Zannan Mustapha ya sa ya sake debo marayu dari uku tare da shirin taimakawa iyayensu mata da tallafin kudi.

Inji Zanna Mustapha bara aka bashi lambar yabon da kudi domin dagewarsa wajen taimakawa marayu. Da ya ga babu abun da zai yi da kudin sai ya kuduri aniyar kara marayu dari uku hade da taimakawa iyayensu mata saboda basu da iyaye maza.

Acewarsa idan aka bar iyayen babu wani taimako ba zasu dinga taimakawa ba su tabbatar 'ya'yansu sun tafi makaranta.

Musa Iyo Kubo kwamishanan ma'aikatar harkokin ilimi na jihar Borno wanda ya wakilci gwamnan wajen bikin ya bayyana matakin da gwamnati ke dauka domin taimakawa dubban marayu dake jihar. Injishi gwamnatin jihar Borno ta yi tanadi na gina makarantu ma marayu. Kawo yanzu akwai makarantu uku da gwamnati ta kafa domin taimakawa marayun.

Makarantar ta Future Prowess tana koyas da karatun boko da na addinin Islama da sana'o'in hannu kamar yadda wakilin Muryar Amurka ya gani a makarantar.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Future Prowess Makarantar Marayu Dake Maiduguri Ta Kara Dalibai Dari Uku - 4' 02"