Kasancewar har yanzu ana ci gaba da samun tashe-tashen hankulan dake da nasaba da zaben da ya gudana a watan Oktoban da ya gabata wanda ake takaddama a kansa.
Hukuncin da kotun kolin Mozambique ta yanke a Litinin din da ta gabata wanda ya tabbatar da nasarar jam'iyyar Frelimo da ta jima a kan mulki ya sabbaba zanga-zangar gama-gari a fadin kasar daga kungiyoyin 'yan adawa da magoya bayansu dake da'awar cewa an tafka magudi a zaben.
A yayin da Rafeal ke zargin zanga-zangar dake faruwa a wajen kurkukun da karfafa gwiwar tarzomar cikinsa, Ministar Shari'a Helena Kida ta shaidawa wata tashar talabijin mai zaman kanta, Miramar TV cewa a kurkukun tarzomar ta samo asali kuma ba ta da alaka da zanga-zangar dake faruwa a wajensa.
"Rikicin da ya biyo bayan tarzomar ya yi sanadiyar mutuwar mutane 33 tare da jikkata wasu 15 a harabar kurkukun," kamar yadda Rafeal ya bayyana a hirarsa da manema labarai.
Har yanzu ba a fayyace bayanan mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba.
Kimanin fursunoni 1, 534 sun arce daga kurkukun sakamakon tarzomar amma an yi nasarar sake kama 150 daga cikinsu, a cewar Rafael, inda ya kara da cewa fursunoni sun yi yunkurin arcewa daga wasu gidajen yarin 2.
Muna cikin damuwa a matsayinmu na kasa, kuma 'yan kasar Mozambique sannan jami'an tsaro," a cewar Rafael, " muna sa ran karuwar laifuffuka nan da sa'o'i 48."
-Reuters