Furannin Kallon Da Suka Fi Farin Jini A Amurka

Furannin kallo na Orchids a gandun furanni ake cewa Botanic Garden.

Amurka kasa ce da mafi yawan mutane ke kaunar Furannin kallo da Ake kira Orchids da turanci A zahiri ma ko a shekarar da ta gabata wannan furanin kallo Orchids ya wuce furnanin kalon Roses farin jini.

Hakan bai zama abin mamaki ba ga Devin Dotson, jami’i mai hulda da jama’a na babban gandun Furanni da ake cewa Botanic Garden dake babban birnin Washington DC. Wanda a kwanan ya taimaka wajen dasa wannan fure na Orchids, wanda yace “Furen kallo na Orchids na da matukar muhimmanci ga Amurkawa, wanda yanzu mutane zasu iya sayensa a duk lokacin da suke so kuma cikin sauki.”

A baya dai suna wahalar samu, har sai bayan da aka kirkiri wani rufaffen gida da za a iya dakon Furen zuwa duk inda ake so, haka kuma ya bayar da damar daukan Furen zuwa ko ina a fadin duniya.

Yanzu haka dai za a iya samun Furen na Orchids a ko wacce nahiya, amma banda nahiyar Antartica, saboda sanyi. Haka kuma Furen shine ya zamanto mafi girma a duniya, dake farantawa Miliyoyin mutane rai idan aka duba siffofinsa da kuma launin kalarsa.