Babban birnin Baijing, na kasar China, ya zama garin da yafi yawan hamshakan masu kudi a duniya. Kimanin shekaru da suka gabata, birnin New York, na kasar Amurka, shine gari da yafi dadewa da tarihin masu kudin duniya suna zama a garin. Babban birnin China, dai shi ke da yawan masu kudin duniya da suka kai sama da mutun 100, haka birnin New York, kuma nada yawan manyan masu kudi na duniya da suka kai yawan mutun 95.
Garin Beijing, dai ya samu daukar wannan kambun ne na gari da yafi yawan mutane masu kudin duniya, bayan rasa kimanin mutane 32 da suke cikin jerin billoniyoyin duniya, a kidayar masu kudin duniya na shekarar 2016.
Garin Moscow, nada yawan masu kudi 66, sai garin Hong Kong, da ke da yawan mutane 64, haka birnin Shanghai, nada mutane 50, sai birnin Landon, da ke da mutane 50, haka birnin Shenzhen, a kasar China, nada mutanr 46, sai garin Mumbai na kasar India, nada mutane 45, shima garin Hangzhou, duk a kasar China, nada mutane 32, garin Paris kuwa nada mutane 30.
Garin Taipei, a kasar Taiwan, nada yawan masu kudin duniya 23, sai garin San Francisco, na kasar Amurka nada yawan mutane 28, kana garin Istanbul, na kasar Turkey, nada yawan mutane 28, haka ma garin Singapore, nada yawan mutane 27, wanda garin Seoul a kasar South Korea, nada yawan mutane 27, sai garin Tokyo, nada mutane 26, haka suma garin Sao Paulo, a kasar Brazil, nada yawan mutane 24, garin Bangkok, na kasar Thailand, nada yawan mutane 24, garin Los Angeles, kuwa nada yawan mutane 21, haka ba a bar garin New Delhi, na kasar India a baya ba inda suke da mutane 20, da suke cikin jerin masu kudi a duniya.