Shugaban Amurka, Barak Obama, na iya zama shugaban kasa na farko da zai zauna a babban birnin tarayyar kasar bayan ya bar mulki.
A lokacin da yake wata ziyarar aiki a Milwaukee ta jihar Wisconsin, shugaban yace a wani bincike da fadar White House ta gudanar, babu wani yanki a cikin Amurka da ya coi moriyar shirin kiwon lafiya ga kowa da kowa da shugaban ya kirkiro kamar wannan yanki na karamar hukumar Milwaukee.
A ganawar da yayi da ‘yan jarida inda aka tambaye shi idan ya gama adadin mulkin shi ina zai koma? Sai yace yana sa ran zai ci gaba da zama a babban birnin tarayya, dalili kuwa shine domin karamar ‘yar shi Sasha, mai shekaru 15, tana makarantar sakandare, kuma yana son ya kyaleta ta kammala karatu a wannan makarantar. Yace cire ta daga wannan makaranta a yanzu na iya gurgunta mata karatu.
To bayan nan fa? Sai yace gaskiya har ya zuwa yanzu, ba su yanke shawarar mai za suyi ba, amma dai ya san cewar yana da bukatar yawon duniya, don kuwa akwai kasashen da yake bukatar ziyarta.