Hari na baya bayan nan shi ne wanda ya faru a yankin kananan hukumomin Takum da Ussa, inda aka kama wasu matan Fulani, batun da shugabanin kungiyoyin Fulani a jihar ke kira da a duba lamarin.
A wajen taron manema labarai da suka kira, shugabanin makiyayan sun nuna bacin ransu kan yadda ake binsu har kasuwanni da ke kan hanyoyi ana kamasu, tamkar kyanwa da bera.
Shugaban kungiyar Fulani ta Tabital Puulaku a jihar, Alhaji Muhammadu, ya bayyana cewa abin da ake yi musu a karamar hukumar Takum ya ta’zzara.
Tuni dai wannan batu ya kai ga uwar kungiyar Miyetti Allah ta kasa, inda shugaban kungiyar mai kula da jihohin arewa maso gabas, Mafindi Umaru Danburam, ya ce da sauran rina a kaba, game da batun neman maslaha a abubuwan da ke faruwa a Taraba.
Sai dai kuma da wakilin Muryar Amurka ya tuntubi shugaban karamar hukumar Takum, Hon. Shiban Tikari cewa ya yi ba haka kawai suke kama Fulanin ba.
Shi ma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP David Misal, wanda ya ce bai da cikakken bayani game da wannan kamu kasancewar baya gari, ya ce matakin na ‘yan sanda bai rasa nasaba da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a wadannan yankuna.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5