Wakilin Fulani a Abuja Adamu Idris wanda wasu 'yan Miyetti Allah suka yiwa muba'aya ya yi shugabancin riko yace gabanin samarma Fulani wurin kiyo zai dakatar da duk wata barazana ga manoma da sauran al'ummar yankin.
Adamu Idris yace yana kiran duk ardodin Fulani su hada kai su goyi bayan gwamnati da shugaban kasa Muhammad Buhari bisa abun dake faruwa da Fulani.
Wani jami'in Miyetti Allah Ardon Rubuci Sanusi Bara yace ba wai sun nuna gazawar Miyetti Allah ta kasa ba ne a karkashin Ardon Zuru Kirwa amma zasu tsaya wajen sauya tsarin Fulanin.
Yace da yake gari ya girma yanzu, ana samun matsaloli da masu kula da muhalli da manoma. Yace duk inda aka je a Abuja, za'a ga an toshe hanyoyin shanu da burtali, kuma kafin makiyayi ya samu ya wuce sai ya shiga gonakin mutane.
Yace samarda burtali ya zama dole domin a samu zaman lafiya. Shanu ba kan titi suke bi ba kamar mota amma kuma ba'a sama suke tafiya ba. Saboda haka ya zama wajibi gwamnati ta samar ma shanu inda zasu ci abinci da shan ruwa. Ban da haka ya nemi a inganta yadda Fulani ke kiwo ya zama na zamani.
Fulanin, a cewar daya daga 'yan tawagar, Abubakar Sulaiman nada gagarumar gudummawa ga tattalin arzikin Najeriya. Yace manomi ma yana bukatar inda shanu suka yi kashi ya zo ya yi shuka a wurin domin shukarsa ta yi kyau. Yace yau a ce nonon shanu da naman shanu basa shiga gari ai tattalin arziki zai samu rauni.
Matsalar satar shanu da hadin bakin wasu bata garin Fulani ke yi, suna zuwa gari suna sayar dasu, na cikin abubuwan da Fulanin suka kuduri aniyar magancewa.
Sarkin Fulanin Dede Umaru Dan Beli yace da zara sun lura da shanun sata zasu zaburar da jami'an tsaro.
Gwamnatin Najeriya ta nuna aniyarta na kawo karshen rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5