Hadin kan kungiyoyin makiyaya da gwamnatin Adamawa ya biyo bayan matsalar yawan satar shanu da kuma yin garkuwa da 'ya'yan Filani da yanzu suna neman su zama ruwan dare gama gari a wasu sassan jihar.
Kungiyar Filanin ta Pulaka tana nata kokarin gano 'ya'yansu ko kuma shanunsu da aka sace..Kungiyar tana gano wasu bata gari tare da sako wadanda aka yi garkuwa dasu ba tare da biyan kudin fansa ba.
Fulanin sun yi murna domin sun ce sun ga anfanin hadin kai na Tabital Pulaku . Suna shiga daji kuma har sun kwato yaransu sama da goma sha daya cikin sati biyu ba tare da biyan fansa ba.
Kugiyar Pulaku ta dade amma yanzu ta samu karbuwa ga wadanda can baya sun ki rungumarta.
Kungiyar ta soma sintiri a wasu kananan hukumomin jihar tare da jami'an tsaro.
Gwamnatin jihar Adamawa ta dauki alkawarin hadin kai da Pulaku domin yakar masu garkuwa da mutane da kuma satar shanu.
Ga karin bayani.