Flato: Shugabannin Kiristocin Arewa Sun Yi Taron Neman Zaman Lafiya

Wasu cikin shugabannin kiristocin arewa (CAN)

Saboda neman zaman lafiya a arewacin Nigeria, shugabannin kungiyar hadin kan kiristoci a jihohi 19 na arewa da Abuja sun fara taron yini biyu a Jos babban birnin jihar Flato domin lalubo dalilan dake haddasa rikici da gano bakin zaren

Kungiyar hadin kan Kirista ko CAN, daga jihohi 19 na arewacin Nigeria da babban birnin tarayya Abuja, ta gudanar da taro kan samun maslaha kan harkokin tsaro da suka addabi yankin arewa.

Taron ya tattaro shugabannin CAN daga jihohin 19 da suka tattauna domin samo musabbabin matsalolin tsaro da matakan da shugabannin addinin kirista zasu dauka wajen kawo karshen matsalolin don samun ci gaba a yankin na arewa.

Rebarand Yakubu Pam, shugaban kungiyar CAN na arewacin Nigeria da Abuja ya bayyana dalilin taron. Ya gayawa wakiliyr Sashen Hausa Zainab Babaji cewa sun kira taron ne domin su tattauna akan abubuwan dake faruwa a arewa, musamman kashe kashe da ake yi. Ya ce abun takaicin shi ne idan sun je kudancin Nigeria za su ga ana ayyukan ci gaba sabanin arewa, inda suke gani ana zubar da jinin mutane, ana rushe rushe da kone kone.

A wurin taron na kwana biyu, Rebarand Pam ya ce kowa ya kawo tashi shawara su hada kai su san inda suka nufa kana su taimakawa gwamnati, da al'umma da sarakuna.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, wanda ya halarci taron, ya ce gwamnati tana kokarin samar da tsaro a kasar. Ya ce gwamnati ta sa abubuawa da yawa a kasa domin tabbatar da zaman lafiya. Za'a sayo makamai tare da kara sojoji. Dangane da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya, Mr. Mustapha ya ce suna rokonsu domin su taimaka. Ya ce lokacin babbar sallah ya kaiwa mai martaba Lamidon Adamawa, da Sarkin Daura, da sarkin Katsina ziyara inda ya rokesu su taimaka ta hanyar fadakar da mutanensu akan bukatar a zauna lafiya.

Wasu mahalarta taron daga sassa daban daban sun yi furuci akan taron. Shugaban matasan CAN na jihar Bauchi ya ce idan shugabannin addinin suka koyas da mutane yadda suka fada a wurin taron, za'a samu fahimta da zaman lafiya.

Ita ma shugabar shashen mata Leah Solomon, dake zaune a jihar Taraba tana fatan abubuwan da suka tattauna a wurin taron su tabbata. Ta kira a ba matasa da mata tallafi domin su samu abun dogaro da kai. A ganinta duk matsalolin za su shude.

Shi ko gwamnan jihar Flato Simon Lalong yace yana da yakinin taron zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro. Ya ce cikin kwanaki biyu na taron za'a duba dalilan matsalolin tare da lalubo bakin zaren magancesu.

A saurari rahoton Zainab Babaji

Your browser doesn’t support HTML5

Plato: Shugabannin Kiristocin Arewa Sun Yi Taron Neman Zaman Lafiya - 3' 59"