Fiye da mutane dari da tamanin sun mutu a Phillipines

Wasu mutane tsaye cikin ambaliyar ruwa a sakamakon hadarin teku a kudancin kasar Phillipines.

Jami’ai a kasar Phillipines sunce hadarin teku ta kashe fiye da mutane dari da tamanin yayinda kimamin dari hudu kuma suka bace a yankin kudancin kasar.

Jami’ai a kasar Phillipines sunce hadarin teku ta kashe fiye da mutane dari da tamanin yayinda kimamin dari hudu kuma suka bace a yankin kudancin kasar.

Cikin dare hadarin teku da aka lakawa suna Washi ta apkawa yankin Mindanao dake kudancin kasar, ta lulube yankin da ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma iska mai karfin gaske,

Shugaban hukumar ceto Benito Ramos ya fada a yau asabar cewa har yanzu jami’ai suna samu bayanai daga yankin, a saboda haka akwai yiwuwar yawan wadanda suka jikatta ya karu.

Hadari tasa dubban mutane sunyi hasara gidajensu. Masu nazarin yanayi suna sa ran gobe Lahadi da dare idan Allah ya kaimu hadari ta sausauto ko kuma ta wuce.