Fiye Da Mutane 100 Ke Fama Da Cutar Kwalara a Jihar Kano

Wata mata da tana fama da cutar kwalara

Dr. Tijani Husseini, mukadashin direktan kiwon lafiyar jama'a da takaita yaduwar cututuka a ma'aikatar lafiya a jihar, yayi bayani cewa sun fara ganin karuwar masu amai da gudawa makonni hudu da suka wuce. Ya kuma ce, a ka'ida idan aka sami wannan yanayi, duk wanda aka tabatar yana da cutar, sai a bi shi zuwa gida domin tsabtace mahalinshi.
Dr. Tijani Husseini, mukadashin direktan kiwon lafiyar jama'a da takaita yaduwar cututuka a Ma'aikatar lafiya a jihar, yayi bayani cewa, sun fara ganin karuwar masu amai da gudawa makonni hudu da suka wuce. Ya kuma ce, a ka'ida idan aka sami wannan yanayi, duk wanda aka tabatar yana da cutar, sai a bi shi zuwa gida domin tsabtace mahalinshi


Dr Hussaini ya bayyana cewa ba kowa ke samun gadon kwanciya a asibiti ba. Yace kusan gadaje 70 dake asibitin Zana duka masu jinyar kwalara ne. Ya kuma bayyana cewa, gadon kwalara yana dabam da sauran gadajen kwantar da marasa lafiya.

Yace gadon ana yi shi ne musaman domin jinyar masu cutar kwalara. Saboda haka ya zama babar kalubala idan aka sami fiye da mutane 70 dake fama da cutar domin babu gadon da za a kwantar da su.

Cutar amai da gudawa cuta ce da idan mutum ya kamu da ita nan da nan sai ya galabaita ruwan jikin shi ya kare, kuma mutum zai iya mutuwa cikin kankanen lokaci.

Your browser doesn’t support HTML5

Cutar Kwalara a Jihar Kano