Baban sakataren maikatan lafiya na jihar Kano, Mallam Garba Shuaibu ya bukaci ma'aikacin lafiya a jihar su jajarce wajen duk abun da aka koya masu, su kuma yi amfani da shi a wuraren ayukan su.
Wakilin kungiyar Clinton Access Initiative, Mallam Lamid Tajudeen yace taron yana da amfani musaman domin samun hanya mafi sauki na kawar da barkewar cutar amai da gudawa.
Shugaban kungiyar Community Health and Research Inititiative (CHARI), Mallan Mohammed Inuwa Shuaibu, yace an zabi Ma'aikatan lafiyan daga kananan hukumomi 45 na jihar.
Yace, "Ya kasance muna cikin wanan hadaka da ake yi tare da gwamnatin jihar Kano da ma'aikatan lafiya, da kuma ita wanan kungiyar duniya mai suna CHARI, domin ayi kokari a gabatar da wata bita da ma'aikatan lafiya akan yadda za ayi kokarin magance wanan larura ta gudawa da yara suke fama da ita, wanda shine baban dalilin da yake sa ake rasa rayuwan kananar yara.