Madam Kala Uma, wata likita a asibiti na sabon gari a Nijar, ta bayyana cewa, suna fama yanzu da cututuka musaman cizon sauro da murar kananan yara. Ta kuma kara da cewa sukan samu mutane masu fama da cuttukan nan kamar guda 200 kullum.
Uma ta ce, “Ana bada magani, ana yin iyakan kokarin da ya kamata. Yara, ana basu magani, manya ma, ana basu magani ldan akwai bukata."
Ganin yadda ya tsananta wanan lokaci, zazzabin cizon sauro ya fi hadabar mata da kananan yara da sukan yi tururuwa a asibiti domin ganin likita, da neman magani.
Likitoci sun bayyana cewa rashin tsabta da kin amfani da gidajen sauro shine ke kawo yawan cuttukan nan. Sun ce mutane suna bukatan sanin amfanin barci cikin gidan sauro, saboda hana kamuwa da zazzabin cizon sauro. Kuma, ya kamata a rika zubar da shara a inda ya kamata.
Ga rahoton da wakilin mu Chuaibu Mani ya aiko daga jihar Maradi.