Fiye Da Mutane 50 Sun Kamu Da Cutar Sankarau a Jigawa

wata mata mara lafiya a gadon asibiti 16, ga Oktoba 2015.

Hukumomin lafiya a jihar Jigawa da ke arewa maso yamamcin Najeriya, sun ce sama da mutane 50 ne suka kamu da cutar sankarau da kuma wasu cutuka na daban a jihar, kuma yanzu haka an tabbatar da mutuwar 14 daga cikinsu.

A cikin makon jiya ne dai aka samu bullar wata cuta da ke saurin hallaka yara a wasu garuruwan jihar Jigawa, amma daga bisani hukumomin jihar suka ce cutar sankarau ce.

Garin Majiya da ke karamar hukumar Taura mai nisan kilo mita kimanin 100 daga birnin Dutse, fadar gwamnatin jihar, shi ne garin da wannan annoba ta sankarau ta munana, inda aka ce yara da dama sun kamu da cutar kuma da yawan su sun mutu.

Wannan dai shi ne karo na karo biyu cikin kasa da watanni 6 da ake samun bullar annobar da ke hallaka mutane da dama a jihar Jigawa.

A tsakanin watan Oktoba zuwa Nuwambar bara, wata cuta ta barke a Kauyen Gidan Dugus, da ke karamar hukumar Dutse wadda ta hallaka kimanin yara 100.

A wancan lokaci al’umar kauyen sun zargi hukumomin jihar Jigawa da sakacin kai musu agajin gaggawa.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Fiye Da Mutane 50 Sun Kamu Da Cutar Sankarau a Jigawa - 3'31"