Fitaccen Mawakin Najeriya Sound Sultan Ya Rasu

Marigayi Sound Sultan

Fitaccen mawakin Najeriya, Olanrewaju Abdul-Ganiu Fasasi wanda aka fi sani da Sound Sultan, ya rasu.

Marigayi fitaccen mawakin wanda ya rera wakar "Jagbajantis" da ya samu karbuwa sosai a shekarun baya ya mutu ne sakamakon jinyar cutar sankarar makogoro yana da shekaru 44 a duniya.

Dan uwan marigayi mawakin, Dakta Kayode Fasasi, ne ya tabbatar da mutuwar Sound Sultan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na yanar gizo ya na mai cewa, a cikin yanayin alhini ne ya ke sanar da mutuwar fitaccen mawakin.

Marigayi Sound Sultan

Mawakin ya bar mata daya, ‘ya’ya 3 da ‘yan uwa a duniya.

Tuni dai mawaka da suka hada da mata da maza suka fara wallafa sakonnin ta’aziyya ga iyalan mamacin a shafukan sada zumunta kamar su Tuwita, Instagram, Facebook da dai suransu.

Fitacciyar mawakiya, Aituaje Iruobe, wacce aka fi sani da suna Waje, ta bayyana kaduwar ta da labarin mutuwar Sound Sultan a shifinta na Instagram.

Mawallafin kafafen sada zumunta Mustapha Tunde wanda aka fi sani da Tunde Ednut, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalin Sound Sultan, ya na mai yin kira ga abokan aikin su, su tallafawa iyalin da mamacin ya bari a duniya.

An haifi Sound Sultan a ranar 27 ga watan Nuwambar shekarar 1977 inda ya mutu sakamakon jinyar cutar dajin makogoro a ranar 11 ga watan Yuli na shekarar 2021 ya na da shekara 44 a duniya.